<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Charles Wesley, John Zundel</author>
<hymn_number>246</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ƙaunar Allah, ba kamarta
 Ko a Sama ko a nan,
 Sai ka cika mana zuciya,
 Sai mu zama cikakku.
 Yesu mai jin tausayinmu,
 Kai mai ƙaunar mutane,
 Ziyarce mu da cetonka,
 Shigo dukan zukata.

[V2]
 2) Sai ka huro mana Ruhu,
 Karfafa mu duk yanzu,
 Kai ne gādonmu, ya Allah,
 Za ka ba mu hutawa.
 Raba mu da son mugunta,
 Kai ne Ruhu, kai ne Rai,
 Farkon kome da cikarsa,
 Allah ne Madauwami.

[V3]
 3) Zo, ya Allah, domin ceto,
 Ba mu duk alherinka,
 Zo da sauri, zo da zama,
 Zauna nan har abada.
 Kai ne kullum mu ke yabo,
 Bautarka ce mu ke so,
 Yin addu'a da sujada
 Sun yi mana daɗi yau.

[V4]
 4) Mai da mu sabuwar halitta,
 Tsarkake mu duka fa
 Har mu ga fansa mai girma
 Wadda ka yi dominmu.
 Sāke mu da darajarka,
 Har mu isa Sama can.
 Za mu rusuna gabanka
 Muna maka godiya,</lyrics>
<title>Ƙaunar Allah, Ba Kamarta LW246</title>
</song>